Babban mai taimakawa shugaban kasa Muhammad Buhari a kan samar da ayyuka da kuma bayar da tallafi, Afolabi Imoukhuede, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kara tsawon wa'adin ma'aikatan N-Power da aka dauka a 2016 zuwa 2018
.
Ya ce duk da wa'adin da aka kayyade na aikin shekaru biyu da za su yi ya cika, gwamnatin tarayya ta kara masu wa'adi domin muhimmiyar gudunmuwar da suke bayarwa a wasu ma'aikatun da suke aiki musamman makarantu.
Da yake zantawa da kamfanin Dillancin Labarai NAN a yau Talata Afolabi Imoukhuede, ya ce wasu ma'aikatan N-Power sun bar aikin a sakamakon samun aikin gwamnati na din-din-din da suka yi a wurare daban-daban
N-Power ta kara tsawon wa'adin ma'aikatan da ta dauka yan 2016
Reviewed by Yakubu Abkr
on
1/29/2019 12:13:00 PM
Rating:
No comments: